Kocin Holland Van Marwijk na tunanin murabus a 2012

Holand
Image caption Spain ce ta doke Holland a wasan karshe a Afrika ta Kudu

Kocin Holland Bert van Marwijk ya ce yana tunanin ajiye mukaminshi ya koma horadda kungiyar kwallon kafa bayan kamalla gasar cin kofin kasashen Turai a 2012.

Wata mujallar Holland ta ambato Marwijk na cewar "ina tunanin zan bar mukami na bayan 2012, lokacin da kwangila ta zata kare, sannan sai in koma wani aikin".

Ya kara da cewar zan koma horadda kungiya amma ba a Holland ba, na fison kungiya a Jamus da Ingila da Spain.

Van Marwijk ya maye gurbin Marco van Basten ne shekaru biyu da suka wuce a matsayin kocin 'Oranje Boys' inda ya kai Holland zuwa wasan karshe na gasar cin kofin duniya a 2010 sannan kuma kasar ta fara da kafar dama a yinkurin neman gurbi a gasar cin kofin kasashen Turai a 2012.