2022:Masu Luwadi kada suyi a Qatar-Blatter

Blater
Image caption A ranar biyu ga watan Disamba ne aka baiwa Qatar

Shugaban hukumar dake kula da kwallon kafa Sepp Blatter ya gargadi 'yan kallo masu luwadi da zasu tafi Qatar don gasar cin kofin duniya a shekara ta 2022 kada suyi harkokinsu a can kasar.

Masu rajin kare hakkin 'yan luwadi sun soki hukuncin baiwa kasar Qatar damar daukar bakuncin gasar saboda a kasar an haramta luwadi.

Amma Blatter cikin wasa ya ce:"bari in fada, masu luwadi sun guji yin harkokinsu a can".

Ya kara da cewar na tabbata za a samu nasara a gasar cin kofin duniya a Qatar ba tare da matsala ba.

Qatar wacce kasar musulunci ce ta bada mamakin samun damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a 2022 bayan ta samu galaba akan Australia da Japan da Koriya ta kudu da Amurka.