Carlos Tevez ya koma horo a Manchester City

tevez da mancini
Image caption Tevez da Mancini sun raba gari

Dan kwallon Manchester City Carlos Tevez wanda ke son ya fice ya koma horo tare da sauran 'yan tawagar a ranar Talata a Carrington.

City taki amince da bukatar Tevez na barin kungiyar, inda yace yanada sabani da sauran mahukunta kulob din.

Kocin kungiyar Roberto Mancini bai halarci horon ba saboda ya tafi Italiya don shirye shiryen fafatawa a gasar Europa da Juventus a ranar Alhamis.

BBC ta fahimci cewar Tevez da Mancini a ranar Juma'a akan makomarshi a Manchester City.

Kungiyar City ta ce ba zata sayarda Tevez a watan Junairu kuma idan har ya daina taka mata leda za ta nemi diyya daga wajenshi.