Fifa:Spain ce farko a yayinda Brazil ta koma ta hudu

iniesta
Image caption Andre Iniesta ne yaci kwallon daya baiwa Spain damar cin kofin

Spain ta kammala bana a matsayin kasa ta farko a jerin manyan kasashe a fagen kwallon kafa a duniya.

Holland wacce ta sha kashi a wajen Spain a wasan karshe na gasar cin kofin duniya itace ta biyu a yayinda Jamus take ta uku sai Brazil ta hudu.

Masar ce ta farko a Afrika amma itace ta tara a duniya sai Ghana ta biyu Afrika sannan ta goma sha shida a duniya.

Najeriya ta koma ta talatin da biyu sai Kamaru ta talatin da bakwai.

Jerin kasashe talatin na farko:

1 Spain 2 Netherlands 3 Germany 4 Brazil 5 Argentina 6 England 7 Uruguay 8 Portugal 9 Egypt 10 Croatia 11 Greece 12 Norway 13 Russia 14 Italy 15 Chile 16 Ghana 17 Slovenia 18 USA 18 France 20 Slovakia 21 Côte d'Ivoire 22 Switzerland 23 Serbia 24 Paraguay 25 Montenegro 26 Australia 27 Mexico 28 Denmark 29 Japan 30 Czech Republic