Gareth Bale ba na sayarwa ba ne - Spurs

Gareth Bale
Image caption Gareth Bale ya taka rawar gani sosai a kakar bana

Shugaban kungiyar Tottenham Daniel Levy ya tabbatarwa magoya bayan kungiyar cewa ba za a sayar da Gareth Bale ba.

Dan wasan mai shekaru 21, wanda kwantiraginsa za ta kare a shekara ta 2014, ya ja hankalin duniya bayanda ya taka rawar gani a kakar bana, musamman ma a gasar zakarun Turai.

"Ba mu yi kama da kungiyar dake sayar da 'yan wasa ba, musamman idan aka yi la'akari da manyan 'yan wasan da muka saya tun bayan zuwa na," kamar yadda Levy ya shaida wa babban taron kungiyar.

"Gareth ya na da yarjejeniya mai tsawo kuma ina tabbatar muku cewa ba zai je ko'ina ba."

Bale ya zira kwallaye tara a bana, biyar a Premier, abinda ya bai wa Spurs damar kasancewa a matsayi na biyar, maki hudu bayan Chelsea wacce ke mataki na hudu.