TP Mazembe ta kafa tarihi

TP Mazembe ta kafa tarihi
Image caption Mulota Kabangu yana murnar kwallon da ya zira a ragar Internacional

Kungiyar TP Mazembe ta zamo ta farko daga Afrika da ta kai wasan karshe a gasar zakarun nahiyoyin duniya wato Club World Cup bayan ta doke Internacional na Brazil da ci 2-0.

Mulota Kabangu ne ya fara zira kwallon farko a minti na 53, kafin Alain Kaluyituka ya zira ta biyu a karshen wasan.

Mai tsaron gidan Mazembe Muteba Kidiaba ya taka rawar gani sosai inda ya hana zakarun nahiyar Kudancin Amurkan zira kwallo ko guda.

Ba wai kawai Mazembe ta zamo ta farko daga Afrika da ta kai wasan karshe a wannan gasa ba ne, har ila yau ita ce ta farko daga wajen Turai da Kudancin Amurka da ta taba kaiwa wannan mataki.

"Mun zo nan ne domin mu wakilci Afrika, kuma dukkan nahiyar na alfahari da kokarin mu," a cewar koci Lamine N'Diaye.