Zambia ta tura tawaga ta musamman zuwa FIFA

Andrew Kamanga
Image caption Andrew Kamanga wanda ke kalubalantar Kalusha Bwalya kan mukamin hukumar FAZ

A ranar Asabar ne gwamnarin kasar Zambia za ta tura tawagar mutane shida zuwa Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA domin tattauna rikicin kwallon kasar.

Tura tawagar ya biyo bayan tattaunawa tsakanin shugaba Rupiah Banda da shugaban FIFA Sepp Blatter.

Shugaban na Zambia ya nemi shugaban FIFA da ya taimaka wajen shawo kan rikicin da ya dabai baye fagen kwallon kasar.

A yanzu Hukumar Kwallon Zambia na da shugabanni biyu wadanda dukkan su ke ikirarin jagorantar Hukumar.

Dan kasuwa Andrew Kamanga ne ke jagorantar bangare guda, yayin da Kalusha Bwalya ke cewa shi ne halartaccen shugaban Hukumar ta (faz).