Manchester City ta buga kunnen doki da Juventus

Jo ne ya zura kwallon da Manchester City ta ci a minti 76 a wasan da ta buga da Juventus a gasar Europa, in da kungiyoyin biyu suka tashi daya da daya.

Manchester City dai ce ta jagoranci rukunin da ta buga a gasar Europa.

An kusan kammala wasa hutun rabin lokaci ne dan wasan Juventus, Niccolo Giannetti ya zurawa Juventus, kwallon ta.

'Yanzu haka dai Manchester City na cikin kungiyoyin 32 da suka tsallake zuwa rukuni na gaba.