Shugaban Inter Milan Moratti ya soki kalaman Benitez

Benitez
Image caption Rafa Benitez na cikin halin kila-wa-kala

Shugaban kungiyar Inter Milan Massimo Moratti ya soki Rafael Benitez akan kalaman mai horadda 'yan kwallon yayi sakamakon nasarar da Inter Milan ta samu a gasar zakarun nahiyoyin duniya.

Bayan da Inter ta casa TP Mazembe daci uku da nema a ranar Asabar, sai Benitez ya bukaci mahukunta kungiyar su nuna mashi goyon baya.

Koda yake dai Moratti ya karyata cewar Benitez ya bata rawarshi da tsalle akan nasarar, amma dai ya ce kamalan kocin basu dace da yanayin da ake ciki ba".

Morrati yace"a halin yanzu magoya bayan Inter na cikin murna".

Amma da aka matsa mashi akan Benitez din sai Moratti yace" ba zan yi magana akan Benitez a irin wannan lokacin ba".