Mancini zai cire Tevez a matsayin kaptin

tevez
Image caption Carlos Tevez zai rasa kambum kaptin

Kocin Manchester City Roberto Mancini zai cire Carlos Tevez a matsayin kaptin din 'yan kwallo.

A ranar Juma'a ne Mancini da Tevez suka gana akan makomar dan kwallon.

City za ta kara da Everton a ranar Litinin, kuma Mancini na tunanin baiwa Kolo Toure ko Vincent Kompany kambum kaptin.

Koda yake dai kocin bai bayyanawa mahukunta kungiyar shawarar daya yanke ba amma dai wasu manyan jami'ai sun nuna cewar Toure ne zai zamo kaptin.

A lokacin Mark Hughes Toure ne kaptin amma sai aka baiwa Tevez kambun daga bisani don dan Argentina ya tsaya a Eastlands. City taki amince da bukatar Tevez a rubuce akan aniyarshi ta barin kungiyar inda mahukunta kungiyar suka ce ba zasu sayarda shi a watan Junairu.