Zan cigaba da murza leda har zuwa 2013-Beckham

Beckham
Image caption David Beckham yana farin jini a Ingila

Tsohon kaptin din Ingila David Beckham ya ce zai cigaba da taka leda daga nan har shekaru biyu zuwa uku masu zuwa kafin yayi ritaya.

Beckham ya bayyana haka ne bayan an bashi kyautar dan kwallo mafi nasara na BBC.

Dan shekaru talatin da biyar din ya kara da cewar sai kwangilarshi ta kare a kungiyar LA Galaxy kafin ya yanke shawarar abinda zai yi anan gaba.

Beckham yace "na yi matukar murnar samun wannan kyautar sannan zan cigaba da abinda nake yi".

Beckham ya kasance dan kwallon da yafi kowanne a tarihi buguwa Ingila kwallon sannan ya lashe gasar premier sau shida da gasar zakarun Turai tare da Manchester United.

Ya kuma lashe gasar La Liga tare da Real Madrid bayan ya koma kungiyar daga United akan pan miliyan 25 sannan daga bisani ya tafi Los Angeles Galaxy sannan sau biyu yana tafiya a matsayin dan kwallon aro zuwa AC Milan.