Bana tunanin ritaya anan kusa-Ferguson

Ferguson
Image caption Sir Alex Ferguson ya lashe gasar premier sau 19

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce baya tunanin yin ritaya anan kusa idan har yana cikin koshin lafiya.

Ferguson ya kasance mai horadda 'yan kwallon United wanda yafi dadewa a tarihi amma dai ya hakikance ba a nan kusa ba yake tunanin barin jan ragamar kungiyar da ya shafe fiye da shekaru ashirin da hudu.

Shekaru tara da suka wuce Ferguson ya yi tunanin yin ritaya amma sai ya canza shawara kuma baya juyayin wannan abu.

Kwadayinshi na samun nasara a fili yake gannin cewar ya jagoranci United ta lashe gasar premier sau 19 kuma a halin yanzu kungiyarshi na daga cikin wadanda ake ganin zasu iya lashe gasar zakarun Turai a nan gaba.

Ferguson ya shaidawa MUTV cewar" kana tsufa kana kara shiga damuwa akan batun ritaya".