Arsenal ce za ta lashe gasar premier

Nasri
Image caption Samir Nasri ya zira kwallaye 12 a kakar wasa ta bana

Dan kwallon Arsenal Samir Nasir ya ce babu tantama a bana kungiyarsu za ta lashe gasar premier a karon faro tun kakar wasa ta 2003-2004.

Duk da cewar kungiyar na bin bayan United da maki biyu amma United nada kwantan wasa, sai dai Nasri ya hakikance suna da karfin samun nasarar daga kofin.

Nasir ya shaidawa jaridar The Sun cewar"ina tunanin gasar bata fi karfinmu ba".

Ya kara da cewar "ina ganin cewar muna da zaratan 'yan kwallon da suka goge wadanda a baya bamu dasu abinda yake bani kwarin gwiwa kenan".

Nasri a kakar wasa ta bana yana haskakawa sosai inda ya zira kwallaye goma sha biyu kawo yanzu kuma aka bashi kyautar gwarzon dan kwallon Faransa na bana.

A cewar Nasri abinda yasa yake haskakawa shine kasancewar Raymond Domenech bai gayyaceshi ba cikin tawagar Faransa zuwa gasar cin kofin duniya, a don haka ya huta sosai.