Mancini na murnar sasantawa da Carlos Tevez

Mancini da Tevez
Image caption Roberto Mancini da Tevez sun maida wukar

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce warware takkadama tsakaninsu da Carlos Tevez shine kadai labari me dadi duk da cewar City ta sha kashi a wajen Everton daci biyu da daya.

Tevez me shekaru 26 ya jaddada sadukarwarshi da biyayya ga kungiyar kwanaki bakwai bayan da ya bada takardarshi ta neman barin kungiyar.

Mancini yace"Abin murna ne saboda mun warware matsalar tare dashi".

Dan kwallon Argentina din zai cigaba rike kambum kaptin din kungiyar wanda a baya ake tananin Kolo Toure zai maye gurbinshi.

Wannan lashe aman da Tevez yayi tabbas zai karawa kocinsa da sauran 'yan kwallon City din.