Shugaban Zambian ya ce FIFA za ta warware matsalar kwallon kasar

banda
Image caption Shugaban Zambia Rupiah Banda

Shugaban kasar Zambia Rupiah Banda ya ce yana murna ganin cewar hukumar kwallon duniya Fifa za ta shawokan matsalolin dake adabbar kwallon kasar.

Fifa ta ce Kalusha Bwalya ne shugaban hukumar kwallon Zambia wato FAZ data sani.

Amma duk da haka Fifa ta ce jami'an FAZ zasu iya kada kuri'ar yanke kauna akan Bwalya idan suna son haka a taron kolinsu a Maris.

Daya bangaren dake karkashin Andrew Kamanga ya riga ya nuna alamun kada kuri'ar cire Bwalya akan mukamin.

Shugaba Banda wanda shine uban kungiyar kwallon kasar ya ce a yanzu akwai alamun cewar za a gudanar da sabon zabe a watan Maris.