Kakuta ya sabunta yarjejeniya da Chelsea

Kakuta ya sabunta yarjejeniya da Chelsea
Image caption Dan wasan yana taka leda sosai a kakar bana

Dan wasan gaba na Chelsea Gael Kakuta, ya sabunta yarjejeniya da kungiyar wacce za ta tsai da shi a kulob din har zuwa shekara ta 2015.

Dan wasan mai shekaru 19, ya zo Chelsea ne a watan Yulin shekara ta 2007, amma sai a watan Nuwamba sannan ya fara taka leda a babbar kungiyar.

Amma yana taka leda sosai a kakar bana, a lokacin da manyan 'yan wasa da dama ke fama da rauni.

"Dole ne na yi kokari na samar wa kaina wuri a cikin 'yan wasa 11 na farko sannan na cimma buri na," kamar yadda ya shaida wa shafin intanet na Chelsea.