Akwai shakku kan makomar Benitez

Akwai shakku kan makomar Benitez
Image caption Al'amura ba sa tafiya daidai a Inter tun lokacin da Benitez ya karbi ragama

Ana ci gaba da nuna shakku kan makomar kocin Inter Milan Rafael Benitez, bayanda Inter Mialn din ta bayyana halin da ake ciki da cewa "yana cike da rudu".

Tsohon kocin na Liverpool shi ne ya jagoranci Inter ta lashe gasar zakarun nahiyoyin duniya a ranar Asabar, sai dai suna mataki na bakwai a gasar Serie A wacce suka lashe a shekaru biyar din da suka wuce.

Benitez ya musanta cewa an kore shi, bayanda wasu rahotanni suka bayyana hakan.

Shugaban Inter Milan Massimo Moratti bai yi karin haske kan halin da ake ciki ba, amma ya ce ana ci gaba da tattaunawa.

"Muna kokarin fahimtar abinda ke akwai, abin ne yana cike da rudu," a cewar Moratti. "Duka abubuwan da ke faruwa sun zo mana da bazata, amma muna duba matakin da za mu dauka."

Amma ko da aka tambaye shi kan ko za su fitar da wata sanarwa a hukumance, sai ya ce: "Ba ma saran sanarda wani abu a yau (ranar Alhamis).