EFCC na binciken Amos Adamu akan shirya wasannin COJA

adamu
Image caption FIFA ta dakatar da Amos Adamu saboda zargin cin hanci da rashawa

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa a Najeriya wato EFCC ta ce ta fara gudanar da binciken da ya shafi cin hanci da rashawa a kan dan kwamitin zartarwar Hukumar kwallon kafa ta duniya da aka dakatar Mr Amos Adamu.

Daya daga cikin abubuwan da hukumar ta ce tana yi masa bincike a kansu shi ne yadda aka kashe tsabar kudi naira miliyon dubu ashirin da hudu a kan wasannin COJA, lokacin da ya shugabanci kwamitin shirya wasannin a shekara ta 2003.

Hukumar EFCCn dai ta bayyana cewa ba wai tana zargin Mr Amos Adamu da yin halin bera game da kudaden da aka kebe wa kwamitin shirya wasannin COJan da ya kai naira miliyon dubu ashirin da hudu, a shekara ta 2003 ba ne, sai dai tana bin kwakkwafin yadda aka kashe su ne.

Kuma bayan wannan ma, a cewar hukumar tana bin kadun zargin da aka yi wa Mr Amos Adamun da ya shafi cin hanci da rashawa a kwamitin zartarwar hukumar kwallon kafa ta duniya, al`amarin da ya yi sanadin dakatar da shi daga kwamitin.