UEFA:Platini zai samu wa'adi na biyu babu hamayya

platini
Image caption Platini ya dare shugabancin Uefa a 2007

Da alamu za a kara zaban Michel Platini a karo na biyu a matsayin shugaban hukumar dake kula da kwallon kafa a turai wato Uefa a watan Maris na badi, saboda a halin yanzu babu wanda ya nuna sha'awar yin takara da shi.

Daga nan zuwa ranar Laraba mai zuwa ne duk wanda keda sha'awara tsayawa takara ya bayyana aniyarshi idan ba haka ba wa'adin ya wuce.

Tsohon kaptin din Faransan mai shekaru 55 a watan Junairun 2007 ne ya dare kujarar shugabancin Uefa bayan ya doke Lennart Johansson.

Sanarwa daga Uefa ta ce "A yau 23 ga watna Disamban 2010, mutum daya ne ya sanarda yin takara wato shugaba mai ci a yanzu Michel Platini wanda ke neman wa'adi na biyu a ofis daga 2011 zuwa 2015".

A ranar 22 ga watan Maris na 2011 ne za a gudanar da sabon zabe don karin wa'adi na biyu.