Blackburn ta nada Steve Kean a matsayin koci

Steve Kean
Image caption Sabon kocin Blackburn Rovers Steve Kean

Balckburn Rovers ta amincewa Steve Kean ya ci gaba da jagorancin kulob din har zuwa karshen kakar wasanni ta bana.

Steve Kean, mai shekaru 43, ya hau matsayin ne a matsayin wucin gadi bayanda shugaban kulob din ya kori Sam Allardyce a ranar 13 Disamba.

"Venkys London Limited - Blackburn Rovers - ya amince ya ci gaba da zama da Steve Kean a matsayin koci har zuwa karshen kakar bana," kamar yadda sanarwar kulob din ta bayyana.

Kean, wanda na cikin masu taimakawa Allardyce, shi ya jagoranci wasan da kungiyar da buga da West Ham inda aka tashi 1-1.

Shugaban kungiyar ya ce ba son yin gaggawa wajen nada zabon koci, amma wannan matakin zai kawo kwanciyar hankali a kulob din.