Chelsea ba ta da karfi kamar daa- Terry

terry da lampard
Image caption John Terry da Frank Lampard sun murmure daga rauni

Kaptin din Chelsea John Terry ya ce yana ganin tawagar 'yan kwallonsu ba suda karfi kamar na kakar wasan data wuce.

Chelsea ta buga wasanni biyar ba tare da samun nasara ba lokacin da Terry da Frank Lampard da Micheal Essien suke jinyar rauni.

Terry yace "a baya muna da manyan 'yan wasa da zamu dinga caccanzasu tare da wasu 'yan kwallon".

Dan shekaru talatin din ya kara da cewar "a yanzu banu da irin haka, muna da matasan 'yan kwallo lokaci yayi da zamu hada kai don cimma burinmu".

Wasan Chelsea da ya kamata ta fafata da Manchester United a dangeshi saboda dusar kankara sannan a ranar litinin mai zuwa zasu kara da Arsenal a filin Emirates. Ana saran Terry zai buga tare da Lampard da kuma Essien a yayinda kungiyar ke kokarin kare kofin data lashe.