An nada Leonardo sabon kocin Inter

An nada Leonardo sabon kocin Inter
Image caption Wannan ne koci na biyu da Inter ta yi a kakar bana

Kungiyar Inter Milan ta nada tsohon kocin AC Milan Leonardo, domin ya maye gurbin Rafael Benitez a matsayin kocinta.

Leonardo Wanda ya lashe gasar cin kofin duniya da Brazil, zai fara aiki a ranar 29 ga watan Disamba har zuwa watan Yulin shekara ta 2012.

An kori Benitez watanni shida bayan nada shi, bayanda ya nemi a ba shi kudi domin sayen 'yan wasa a watan Janairu.

"Mun yi amannar cewa Leonardo yana da kwarewa wacce za ta kai kulob din ga gaci," a cewar shafin intanet na Inter Milan.

Sai dai Leonardo bai taba yin aikin koci ba sai na shekara dayan da ya shafe a AC Milan a kakar bara.