Wasannin Premier: Dusar kankara na kawo cikas

David Moyes
Image caption Manajan kungiyar kwallon kafa ta Everton, David Moyes

Matsanaciyar zubar dusar kankara na ci gaba da kawo tsaiko a wasannin Premier na Ingila.

Daga cikin wasannin da ake dage saboda zubar dusar kankarar har da wasan Everton da Birmingham.

A wata sanarwa da suka wallafa a shafinsu na intanet, Everton sun ce bututan da ke filin wasansu sun daskare kuma da dama daga cikinsu sun ma fashe cikin daren jajibirin Kirsimeti.

"ma'aikatan filin wasanmu da jami'an kula da lafiya sun yi ta aiki ba ji ba gani, to amma saboda tabarbarewar yanayi, kuma don kiyaye lafiyar jama'a, ya zama tilas mu dakatar da wannan wasa; mun yi hakan ne kuwa ba da son ran mu ba", inji sanarwar ta Everton.

Hakazalika, an dage wasan da aka shirya gudanarwa yau Lahadi tsakanin kungiyar Blackpool da Liverpool saboda kankara ta lullube filin wasa na Bloomfield Road.