Karawar Arsenal da Chelsea

Filin wasa na Emirates
Image caption Filin wasa na Emirates

Dage wasan Arsenal da Stoke a karshen makon da ya gabata ya zamowa kulob din jinkirin alheri, domin kuwa ya baiwa Lukasz Fabianski da Abou Diaby dama su murmure sosai.

Manajan kulob din, Arsene Wenger ya tabbatar da cewa Thomas Vermaelen zai ci gaba da zama a benci har zuwa karshen watan Janairu.

Su kuwa Chelsea, a karo na farko tun watan Agustan da ya gabata, za su mayar da Frank Lampard cikin jerin 'yan wasan da za su buga a rabin lokaci na farko.

'Yan wasan Chelsea, Alex, Yossi Benayoun da Yuri Zhirkov ba za su shiga fili ba saboda rauni.

Da karfe takwas na dare agogon GMT ne dai, wato karfe tara agogon Najeriya da Nijar, Aresnal da Chelsea za su raba raini a filin wasa na Emirates.

Wannan ce karawa ta dari da saba'in da biyar a tarihin karawa tsakanin kungiyoyin biyu masu tsananin adawa da juna.

Kyaftin din Arsenal, Cesc Fabregas, ya yarda cewa kulob dinsa ba su da kwarin gwiwa kuma suna cike da fargabar shan kaye a wasansu da Manchester United.

Babu kulob din da ya ke tayar da hankalin Arsenal kamar Chelsea; ga shi kuwa Didier Drogba ya san lagwansu fiye da ko wanne dan wasa.

A karawa goma sha dayan da aka yi tsakanin Arsenal da Chelsea Drogba ya ci kwallaye goma sha uku.

Sai dai arangamar da Drogba ya yi da zazzabin maleriya ta dan rage masa karsashi; hakan kuma ya zo daidai lokacin da kulob din na Chelsea ya shafe wata guda ba tare da ya yi nasara a wasa ko daya ba.

Chelsea ba su samu damar nuna cewa sun farfado a gasar Premier ba saboda dage wasansu da Manchester United a makon jiya.