Dan kwallon Togo Boukari ya koma Rennes

boukari
Image caption Dan Togo Razak Boukari

Dan kwallon Togo Razak Boukari ya koma kungiyar Rennes ta Faransa daga Lens.

A halin yanzu Rennes ce ta biyu akan tebur inda take bin Lille.

Boukari ya koma Lens ne a shekara ta 2006 kuma a yanzu ya kulla yarjejeniya da Rennes din ne ta shekaru hudu masu zuwa.

Boukari yace"nayi matukar murnar kulla yarjejeniya da Rennes, na yanke shawarar canza sheka tuntuni".