Na tsallake rijiya da baya-Ancelotti

ancelotti
Image caption Carlo Ancelotti na fuskantar matsin lamba

Kocin Chelsea Carlo Anceloti ya amince cewar ya yi matukar sa'a da har yanzu shike jagorantar kungiyar duk da mummunar rawar da suke takawa.

Chelsea wacce ta lashe gasar premier a bara a wannan karon ta samu galaba ne a wasa daya tal cikin takwas sannan itace ta biyar akan tebur.

Yace"na san cewar tuni da an kore ni idan da wasu masu horadda 'yan kwallon ne suke samun irin wannan sakamakon, a gaskiya nayi sa'a sosai".

Ganin irin rudun da kungiyar ta shiga a yanzu, Ancelotti na kokarin yadda 'yan wasanshi zasu cigaba da irin salon wasan da suka soma a farko kakar wasa ta bana.

Kafin wasan da Chelsea za ta kara da Wolves a ranar Laraba, Manchester United ce ke jan ragama inda tafi Chelsea din da maki tara.