Beckham na tattaunawa da LA Galaxy akan zuwa Ingila

beckham
Image caption Beckham ya yi horo da Spurs yana karami

David Beckham na tattaunawa da Los Angeles Galaxy akan zuwanshi gasar Premier na wucin gadi, kuma ana saran Tottenham ce za ta same shi.

Akwai alamun Galaxy zata saki Beckham amma dai horo kawai za'a barshi yayi ba zai buga gasa ba.

Blackburn da Newcastle suma sun nuna kwadayinsu akan dan kwallon amma dai zuwa Spurs inda Beckham yayi horo a matsayin dan makaranta shine inda ake gannin tsohon kaptin din Ingila zai je.

Har yanzu ana sasantawa akan batun tsakanin wakilin Beckham da kuma Galaxy.

Amma dai idan har aka kulla yarjejeniya tsakanin Tottenham ba tare wasu sharuda, tabbas Beckham zai iya kara da tsohuwar kungiyar Manchester United a ranar 16 ga watan Junairu.