Ba zan sayi sabon dan kwallo ba-Mourinho

mourinho
Image caption Jose Mourinho na kokarin kamo Barca

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya ce akwai shakku kungiyar zata sayi sabon dan kwallo don maye gurbin dan Argentina Gonzalo Higuain wanda za a yiwa tiyata.

Mourinho yace Karim Benzema shine kadai ya rage a gaban Real abinda kuma zai yi jefa kungiyar cikin matsala.

Kocin ya tattauna da shugaban Real Florentino Perez akan sayo sabon dan kwallo amma har yanzu bai ce komai ba akan batun.

Mourinho yace"bana tunanin zamu samu sabon dan kwallo".

Higuain zai shafe watanni biyu baya taka leda saboda wannan tiyatar.

A halin yanzu Real Madrid ce ta biyu akan teburin gasar La Liga inda Barcelona ke jan ragama.