Tunisia ta nada Faouzi Benzarti a matsayin koci

Benzarti
Image caption Faouzi Benzarti nada babban aiki a gabanshi

Tunisia ta kara nada Faouzi Benzarti a matsayin kocin manyan 'yan kwallon kasar.

Wannan ne karo na biyu da aka nada Benzarti bayan ya jagoranci Carthage Eagles a gasar cin kofin kasashen Afrika a Angola a 2010.

A watan daya gabata ne Bertrand Marchand ya sauka daga mukamin kocin kasar bayan 'yan kwallonshi sun sha kashi a wajen Botswana a wasan share fage na cancantar buga gasar cin kofin kasashen Afrika a badi.

Benzarti zai iya cigaba da jagorantar kasar idan har ta tsallake zuwa gasar kofin Afrika a badi.

A halin yanzu Tunisia ce ta biyu akan tebur rukunin K, a gasar da za ayi a kasashen Equatorial Guinea da Gabon.