Liverpool na tunanin korar Hodgson

hodgson
Image caption Roy Hodgson ya kasa taka rawar gani a Liverpool

Masu mallakar kungiyar Liverpool na tunanin korar Roy Hodgson a matsayin koci, amma dai ba a yanke shawara akan hakan ba.

Liverpool ce ta goma sha biyu akan teburin gasar Premier bayan ta sha kashi a wajen Blackburn daci uku da daya a ranar Laraba, kuma an doke ta sau tara kenan cikin karawa 20 a gasar.

A yayinda aka kamalla rabin takarar lashe gasar, Liverpool ta wuce rukunin kungiyoyin da zasu nitse ne da maki hudu kacal.

A ranar Alhamis ne ake saran kungiyar za ta fidda sanarwa akan batun kocin.

Hodgson ya bar Fulham ne don maye gurbin Rafael Benitez a Anfield a watan Yuli .