Kasashen larabawa na kara karfi a kwallon duniya

fifa
Image caption Tambarin Fifa

Kasashen Larabawa na kara karfi a harkar kwallon kafa a duniya bayan da aka zabi Yarima Ali Bin Al-Hussein na Jordan a matsayin mamba a kwamitin gudanarwa na hukumar kwallon duniya wato Fifa.

Al-Hussien ya doke Chung Mong joon na Koriya ta Kudu a zaben da aka gudanar a birnin Doha na Qatar.

Wannan zaben na zuwa ne kusan wata guda bayan da aka baiwa Qatar damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2022. Chung Mong joon ya shafe shekaru goma sha shida akan kujerar shugabanci,kuma wannan zaben yasa Al Hussein mai shekaru 35 da haihuwa ya zama mafi karancin shekaru a kwamitin gudanarwa na Fifa.

A taron na yau kuma an kara zaben Mohamed bin Hamman a matsayin shugaban hukumar kwallon nahiyar Asiya a karo na uku.