Arsenal ta amince da jan katin Sagna

Image caption Bacary Sagna

Arsenal ba za ta samu amfani da dan wasan bayan ta ba, wato Bacary Sagna na tsawon wasanni uku bayan an nuna mishi jan kanti a wasan da kungiyar ta buga canjaras da Manchester City.

A nunawa dan wasan jan kanti ne bayan wata 'yar dambarwa da suka yi da dan wasan City Pablo Zabaleta.

"Na ga yadda al'amarin ya faru. Babu yadda za mu kalabulanci katin, Jan kati ne kuma mun amince da shi". In ji kocin Arsenal, Arsene Wenger.

"Ya fusata ne, kuma ya kasa jurewa."

City dai ta tabbatar da cewar za ta kalubalanci sallaman da akayiwa dan wasanta Zabaleta a dambarwar.