Blatter ya ce za'a buga gasar cin kofin duniya a Junairu

Image caption Sepp Blatter

Shugaban hukumar Fifa Sepp Blatter ya ce yana sa ran za'a buga gasar cin kofin duniya wanda za'a shirya a kasar Qatar a shekarar 2022 a watan junairu saboda matsananci zafi da ake yi a lokacin bazara a kasar.

Ana dai shirya gasar ne a watannin Yuni da Yuli amma ana samun matsananci zafi a kasar Qatar a wannan lokacin.

Dayake jawabi a birnin Doha, babban birnin Qatar, Blatter ya ce: "Ina sa ran zamu shirya gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 a lokacin hunturu."

"Nan da shekaru goma sha daya ne za'a shirya gasar, kuma zamu zabi lokacin da ya dace mu shirya ta saboda yanayin zafi a Qatar."