Tsohon dan wasan Najeriya Uche Okafor ya rataye kansa

Image caption Uche Okafor

Tsohon dan wasan bayan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles, Uche Okafor ya rataye kansa a gidansa dake Dallas a Amurka.

Tsohon dan wasan na cikin tawagar da ta lashe gasar cin kofin Afrika da Najeriya ta lashe a shekarar 1994, kuma harwa yau yana cikin tawagar Najeriya da suka buga a gasar cin kofin duniya a Amurka a shekarar 1994.

Dan wasan ya taka wa Najeriya leda sau talatin da hudu.

Har yanzu dai mahukunta a Amurka ba su bayyana dalilin da yasa dan wasan ya kashe kansa ba.