Beckham ya tafi Tottenham na wucin gadi

Tsohon kaptin din Ingila David Beckham ya amince yayi horo tare da Tottenham har zuwa ranar goma ga watan Fabarairu amma ba zai buga wasa a gasar premier ba.

BBC ta fahimci cewar tsarin inshoran dan kwallon a LA Galaxy bai bashi damar ya taka leda a gasa ba.

Kungiyar ta ce tana murna cewar David Beckham zai yi hori da tawagar ta.

Tunda farko kocin Spurs Harry Redknapp ya ce"tsarin yarjejeniyar babu karfi".

Galaxy ta bukaci a biyata inshora saboda Beckham ya kamu da rauni a lokacin da yake wucin gadi a AC Milan.

Wannan raunin ne kuma ya hana tsohon dan kwallon Manchester United ba buga gasar cin kofin duniya ba a bara.