Caf U17: Rwanda ta fara da kafar dama

caf
Image caption Tambarin CAF

Rwanda mai masaukin baki ta fara gasar cin kofin Afrika ta 'yan kasada shekaru 17 da kafar dama, bayan ta doke Burkina Faso daci biyu da daya a ranar Asabar.

Cikin minti uku da farawa dan Rwanda Faustin Usengimana ya bude fagen a yayinda Tibingana Mwesigye yaci na biyu sai kuma Faisal Ouedraogo daya ciwa Burkina Faso kwallo guda.

A daya wasan kuwa Masar ta doke Senegal itama daci biyu da daya.

Sai a ranar Talata mai zuwa Masar zata buga wasanta na biyu tsakaninta Rwanda sai kuma Burkina Faso ta hadu da Senegal.