An nada Lito Vidigal a matsayin kocin 'yan kwallon Angola.

vidgal
Image caption Sabon kocin Angola Lito Vidigal

An nada Lito Vidigal a matsayin sabon kocin tawagar 'yan kwallon kasar Angola.

Dan shekaru arba'in da daya ya kulla yarjejeniya ta shekaru biyu da Palancas Negras.

Ya maye gurbin Zeca Amaral wanda aka nada kocin riko a baya.

Shugaban hukumar kwallon Angola Justino Fernandes ya ce "Zeca Amaral ya bukaci ya bar mukamin don ya koma wata cibiyar".

Vidigal tun bayan da yayi ritaya a kwallo a shekara ta 2004 yake horadda 'yan kwallo a Portugal.

A baya ya jagoranci Uniao Leiria da Portimonense da Ribeirao da kuma kungiyar Estrela Amadora.