UEFA za ta hukunta kungiyoyin dake saba ka'idar kashe kudi

platini
Image caption Shugaban Uefa Michel Platini

Shugaban hukumar dake kula da kwallon Turai wato UEFA Michel Platini yace duk wata kungiyar data ki bin ka'ida wajen kashe kudi, tabbas za a hukuntata.

Platini ya ce UEFA zata iya dage kulob daga shiga gasar zakarun Turai idan har aka kama klub da saba ka'ida wajen kashe kudade.

Platini yace kungiyoyin da aka kama da laifi zasu gani a kwaryarsu.

UEFA ta duba yadda kungiyoyi 655 suka kasafta kudadensu kuma an gano a shekara ta 2009 fiye da rabi sun fadi babu riba.

Gibin da suka samu yakai na dala biliyan daya da rabi.

Shugaban kungiyar kulob kulob na Turai Karl-Heinz Rummenigge yace dole ne kungiyoyi subi doka domin cire su a gasar zakarun Turai zai haifar masu da babbar matsala.