Amos Adamu na kokarin sake komawa Fifa

amos
Image caption An cire Amos Adamu a Fifa saboda zargin cin hanci da rashawa

Tsohon babban jami'in Fifa wato dan Najeriya Amos Adamu na kokarin sake kwato mukaminshi a kwamitin gudanarwar Fifa.

A watan Nuwamba bara ne aka dakatar da Adamu na tsawon shekaru uku bayan da aka kamashi da laifin sayarda kuri'arshi ta zaben kasar da za a baiwa damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya.

Hukumar dake kula da gasar kwallon Afrika wato Caf ta ce Amos Adamu da Jacques Anouma duk sun kara mika takardar sake neman mukamansu.

A wata mai zuwa ne aka saran za a sake takarar kujerar Adamu.

Idan har Adamu ya kasa samun nasarar kalubalantar dakatarwar da Fifa ta yi mashi, to Ibrahim Galadima ne zai yi takara a madadin Najeriya.