Dan Kamaru Geremi Njitap ya bar Larissa

geremi
Image caption Geremi Njitap

Kungiyar Larissa ta kasar Girka ta amincewa dan kwallon Kamaru Geremi Njitap ya tafi.

Sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Laraba ta ce"kulob din ya ji dadin aiki tare da Geremi amma kash ya kasa gano sallon kwallon Girka"

A watan Agustan daya wuce, an yita murnar zuwan Geremi kungiyar a matsayin babban dan kwallon daya shahara.

Amma dai wasanni goma kawai ya bugawa kungiyar a kakar wasa ta bana.

A baya dai Geremi ya taka leda a Real Madrid da Chelsea kuma ya bugawa Kamaru wasanninta uku a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu a shekara ta 2010.