Ghana ce zata lashe gasar kofin Afrika-Stevanovic

goran
Image caption Sabon kocin Ghana Goran Stevanovic

Sabon kocin Ghana Goran Stevanovic ya sha alwashin lashe gasar cin kofin kasashen Afrika ta reda Black Stars a karon farko tun shekarar 1982.

Dan Serbiyan me shakaru 44 wanda a ranar Laraba aka gabatar dashi a bainar jama'a, ya ce yana da kwarewar da zata kai Ghana ga nasara.

Tsohon kocin Partizan Belgrade din ya kulla yarjejeniya ta shekaru biyu wacce za a iya sabuntawa sannan matakin farko shine ya tsallakar da Ghana zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a 2012.

Stevanovic a zarihi yanada damar lashe gasar Afrika sau biyu a cikin wannan yarjejeniyar ta shi wato a 2012 da 2013.

Wasan da kocin zai jagoranta na farko shine tsakanin Ghana da wata kasar da ba a bayyana ba na sada zumunci a ranar tara ga watan Fabarairu kafin su fafata da Congo a wasan cancantar buga gasar kasashen Afrika a ranar 27 ga watan Maris.

Daga bisani kuma Ghana ta hadu da Ingila a filin Wembley don wasan sada zumunci.