UEFA za ta fara bada sabuwar kyauta ga 'yan kwallo

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Turai UEFA ta ce zata kirkiro da sabuwar kyauta ga 'yan kwallon Turai don maye gurbin Ballon d'Or wacce mujallar Faransa ke badawa.

Shugaban Uefa Michel Platini wanda ya bayyana haka a hira da wata jarida ya ce sun dauki matakin ne saboda Ballon d'Or sun hade da Fifa sun koma bada kyautar a tare.

A cewarshi za a dunga bada kyautar ce a watan Agusta na duk shekara a birnin Monaco a ranar da za a rarraba yadda kasashe zasu fafata da junansu a gasar zakarun Turai.

Kasashen dake da wakilci a hukumar Uefa ne zasu zabi gwarzon dan kwallon na Turai, tare da 'yan jarida da kuma masu horadda 'yan kwallo.

A ranar Litinin data wuce ne aka baiwa Lionel Messi kyautar gwarzon dan kwallon duniya na Fifa tare hadin gwiwar Ballon d'Or.