Santa Cruz da Wright-Phillips zasu bar City-Mancini

cruz
Image caption Wright Phillips da Santa Cruz

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya tabbatar cewa Roque Santa Cruz da Shaun Wright-Phillips zasu bar kungiyar a 'yan kwanaki masu zuwa.

Santa Cruz dan kasar Paraguay ana saran zai koma Blackburn wato kungiyar daya fara takawa leda a Ingila.

Shi kuwa Wright-Phillips zai koma Fulham ko Birmingham ko kuma West Ham ne.

Mancini ya kara da cewar baya son ya bar Emmanuel Adebayor ya tafi har sai ya samu bayani ko Mario Balotelli na bukatar tiyata a gwiwa ko kuma a'a.

Santa Cruz da Wright-Phillips duk sun je City ne lokacin Mark Hughes amma tun zuwan Mancini ya daina sasu a cikin wasa. A ranar Laraba ne City ta saki Wayne Bridge ya koma West Ham.