An dakatar da Ghana daga shiga harkar Olympics

rogge
Image caption Shugaban IOC Jacques Rogge

Shigar kasar Ghana cikin gasar Olympics na 2012 a London ya yi karo da cikas, bayan da kwamitin Olympics na duniya IOC ya dakatar da kasar.

Kwamitin IOC ya dauki matakin ne saboda katsalandan na siyasa daga bangaren gwamnati a harkokin kwamitin Olympics na Ghana.

Shugaban IOC Jacques Rogge ya ce dokokin wasannin Ghana basu mutunta harkokin Olympics.

Dakatar da Ghana ma nufin cewar za a daina bata tallafi daga IOC sannan kuma kasar ba zata shiga cikin gasar Olmpics a 2012 ba.

Rogge yace"an yita alkawarin sauya dokoki amma har yanzu babu abinda ya canza".

Za a iya dage Ghana idan ta amince da dokokin IOC kuma hakan zai tabbatar da kwamitin olympics na Ghana zai zama mai cin gashin kansa tun bayan da ya shiga rudu a shekara ta 2009.