Aston Villa na zawarcin dan Kamaru Jean Makoun

makoun
Image caption Jean Makoun

Kocin Aston Villa Gerard Houllier na zawarcin dan kwallon Lyon wato dan Kamaru Jean Makoun.

Makoun mai shekaru ashirin da bakwai ana saran Villa za ta bada akalla pan miliyan akan dan kwallon.

Houllier ya ce "muna bukatarshi saboda gogaggen dan kwallo ne".

Ya kara da cewar"ya iya wasa sosai kuma a wannan lokacin zai taimaka mana sosai".

Houllier na kokarin kara karfin tawagarshi don tsallakewa daga rukunin kungiyoyi da zasu nitse daga premierhip zuwa championship.