Rashin kwarin gwiwa ne matsalar Chelsea - Lampard

Frank Lampard
Image caption Lampard ya dade ba ya taka leda saboda rauni

Dan wasan Chelsea Frank Lampard ya ce kungiyar na fuskantar matsalar rashin kwarin gwiwa wacce ta jefa su a halin da su ke ciki a yanzu.

Lampard ya ce wannan yanayi ya yi daidai da na shekara ta 2009, lokacin da Luiz Felipe Scolari ke jagorantar kungiyar.

Dan wasan na Ingila ya ce: "A yanzu ba mu da tabbas kan abin da zai faru idan muka fita fagen daga".

"Wannan ya yi kama da karshen lokacin Scolari. Ba mu da kwarin gwiwa a duk lokacin da muke wasa".

Kocin Chelsea na yanzu Carlo Ancelotti, yana cikin matsin lamba bayanda kungiyar ke fuskantar koma baya, bayanda a baya ta fara haskaka wa.