Chelsea ta soma shan kwana-Ancelotti

ancelotti
Image caption Hankalin Ancelotti ya soma kwantawa

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce kungiyar tash kwana bayan doke Blackburn Rovers data yi daci biyu da nema a filin Stamford Bridge.

Wannan nasarar itace ta biyu da Chelsea ta samu cikin wasannin gasar premier goma.

Ancelotti ya shaidawa BBC cewar: "Wannan nasarar nada matukar mahimmanci kuma mun wuce zamanin matsalarmu kenan".

Sakamakon wasu daga cikin wasannin premier:

* Manchester City 4 - 3 Wolverhampton * Stoke City 2 - 0 Bolton Wanderers * West Bromwich 3 - 2 Blackpool * Wigan Athletic 1 - 1 Fulham * West Ham United 0 - 3 Arsenal