Inter Milan ta gano bakin zaren karkashin Leonardo

leonardo
Image caption Kocin Inter Leonardo

Inter Milan karkashin jagorancin dan Brazil Leonardo ta fara gano bakin zaren inda ta samu nasara a wasanni hudu a jere tun bayan korar Rafael Benitez.

Inter a ranar Asabar ta lallasa Bologna daci hudu da daya inda Samuel Eto'o ya zira kwallaye biyu.

Sakamakon sauran karawar da akayi a gasar Serie A:

* Cagliari 3 - 1 Palermo * Juventus 2 - 1 Bari * Catania 1 - 1 Chievo * Brescia 2 - 0 Parma * Cesena 0 - 1 Roma * Lazio 1 - 0 Sampdoria * Genoa 2 - 4 Udinese