Dan Kamaru Jean Makoun ya koma Aston Villa akan pan miliyan shida.

jean
Image caption Makoun na murnar komawa Villa

Dan kwallon Kamaru Jean Makoun ya sanya hannu a yarjejeniya tsakaninshi da Aston Villa akan pan miliyan shida.

Dan wasan mai shekaru ashirin da bakwai ya amince ya taka leda a Villa park na shekaru uku da rabi.

Makoun ya bayyana cewar "nayi farin cikin hadewa da wannan babban kulob"

Ana saran Makoun zai fara taka leda a karshen wannan watan idan aka bashi takardar izinin fara buga kwallo a Ingila.

A halin yanzu Villa ce ta goma sha takwas akan teburin gasar premier kuma kocin kungiyar Gerrard Houllier na kokarin kara karfin tawagarshi.