Dan Afrika ta Kudu Tshabalala zai koma Nottingham

Tshabalala
Image caption Siphiwe Tshabalala

Dan kwallon Afrika ta Kudu wanda ya haskaka a gasar cin kofin duniya Siphiwe Tshabalala na shirin komawa kungiyar Nottingham Forest.

Dan kwallon mai shekaru ashirin da shida ya samu kungiyoyi da dama da suka nuna sha'awarshi tun bayan daya zira kwallon farko a gasar cin kofin duniya tsakaninta da Mexico.

Tshabalala zai isa Forest a ranar Litinin yanasaran zai bar Kaizer Chiefs akan watakila pan miliyan daya da rabi.

Wakilin dan kwallon Jazzman Mahlakgane ya tabbatar da cewa akwai kungiyoyi a Ingila wanda suke kokarin siyanshi.